‘Yan kungiyar Boko Haram, sun kai wani hari a wani gari mai suna Bia a cikin karamar hukumar Kolofata, a kasar kamaru a daren jiya.
Mutane goma sha biyu ne suka rasa rayukansu a sakamakon wannan mummunar hari da ‘yan kungiyar ta Boko Haram, suka kai kasar Kamaru, an dai samu saukin hare-haren ‘yan kungiyar kafi wannan harin na baya-bayan nan.
Da yake yiwa wakilin Muryar Amurka bayani kan hari da 'yan Boko Haram, suka kai kasar ta Kamaru, Malam Liman Maigari, yace tabas karfin 'yan kungiyar yanzu kam ya kare kuma suna fama da yunwa da kuma rashin abinci.
Yanzu haka jihohi goma na kasar Kamaru, suna tara kudade da abinci saboda turawa Sojojin dake faggen fama a jihar arewa mai nisa. Jihar arewa kawai ta tara sama da miliyan tasa’in da abinci, wanda tuna Gwamnar jihar ya mika ga hukumomin Sojin kasar.