Ranar Talata ne ‘yan sandan garin Rajura dake Indiya suka kame wani tsuntsun Aku, kan laifin cin mutuncin wata tsahuwa mai shekaru 80 da haihuwa.
Kamar yadda gidan jaridar Z news ya fitar da rahotan cewa matar mai suna Janabi ta shigar da kara ofishin ‘yan sanda inda ta bayyana yadda tsuntsuwar ke cin zarafin ta, bayan da mai tsuntsuwar ya koya mata abinda zata rika gayawa tsohuwar a duk lokacin da take wucewa ta kofar gidan.
Suresh shi ne mamallakin Akun mai suna Hariyal, kuma yana fuskantar tuhuma kan wannan zargi da ake masa, a shekarun baya da suka wuce an sami rashin jituwa tsakanin Janabi da Suresh, tun daga wannan lokaci ya koyawa Akun sa duk lokacin da ya ga matar zata wuce ta kofar gidan daya ringa gaya mata wasu kalmomi irin na zagi da basu dace ba.
Janabi tace ta kai karan kasancewar kwashe shekaru biyu tana fuskantar cin zarafi daga tsuntsuwar, ‘yan sanda dai sun kwace tsuntsunwar daga hannun mai ita suna kuma binciken lamarin, daga bayane aka saki Akun bayan da ‘yan sanda suka kawo shi cikin keji amma baice uffan ba ga matar, kuma babu wata wani tsarin doka da ya kunshi hukuncin da za’a yankewa tsuntsu bayan da ya zagi mutum.