A bangaren wasannin Olympic da ake kuwa, ‘yar wasan juya jiki ta Amurka Simone Biles, yanzu haka a hukumance ta zamanto shahararriyar ‘yar wasan juya jiki ta duniya.
A jiya Alhamis ne ta lashe wasan juya jiki na mata, yayin da takwararta wadda suke kungiya ‘daya Aly Raisman ta lashe lambar yabo ta Silver. Sai kuma ‘yar wasan kasar Rasha Aliya Mustafina ta sami lambar Bronze.
Biles ‘yar shekaru 19 da haihuwa yanzu dai itace ‘yar wasan Amurka ta hudu da ta taba lashe wasannin juya jiki baki ‘daya, inda ta zama shahararriyar ‘yar wasan juya jiki.
Shahararren ‘dan wasan ninkayar nan na Amurka Micheal Phelps, ya lashe babbar lambar yabo ta gold a karo na 22 a rayuwarsa, a ninkaya mai nisan mita 200 jiya Alhamis.
Phelps wanda yanzu haka ya lashe lambar gold har uku a Rio, wanda yayi ninkaya kusa da dadadden abokin karawarsa Ryan Lochte. Sai dai Lochte baiyi ninkayar da ta kai ta Phelps ba, kuma ya zo na biyar a gasar
Kosuke Hagino dan wasan kasar Japan, wanda a baya ya lashe wasan ninkaya mai nisan mita 400, yanzu shine ya zo na biyu, sai kuma Wang Shun daga China yazo na uku.