Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Lashe Lambobin Zinare - Najeriya

Men compete in the Muscle Beach Independence Day bodybuilding contest on Venice Beach in Los Angeles, California, July 4, 2013. REUTERS/Lucy Nicholson (UNITED STATES - Tags: SOCIETY SPORT) - RTX11CYF
Men compete in the Muscle Beach Independence Day bodybuilding contest on Venice Beach in Los Angeles, California, July 4, 2013. REUTERS/Lucy Nicholson (UNITED STATES - Tags: SOCIETY SPORT) - RTX11CYF

Tawagar ‘yan wasan Najeriya masu daga kayan nauyi, ta sha alwashin za ta lashe akalla lambobin zinare goma a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da ake yi a Congo Brazzaville na kasashen Africa.

Shugaban tsare-tsare hukumar da ke kula da wasan daga kayan nauyi, a Najeriya, Samuel Ekeoma, ya ce ya na da kwarin gwiwa ‘yan wasan Najeriya za su haska a karshen wasannin.

A cewar Ekoema, Najeria ta kafa tarihin lashe kyaututtuka akalla biyar a bangaren daga kayan nauyi, inda ya ba da misali da ‘yar wasa Lovelina Obiji mai daga nauyin kilo 88 da Ben Nsini mai daga nauyin kilo 41 da Kehinde Paul mai daga nauyin kilo 65 sai kuma Ezuruike Rowland mai daga nauyin kilo 54 da kuma Pracious Orji mai daga nauyin sama da kilo 86.

Za Mu Lashe Kyautukan Zinare - Najeriya - 0'48"

XS
SM
MD
LG