Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAUREN MATASA: Boye Wa Juna Sirrin Wayar Hannu Tsakanin Ma'aurata


Kamar yadda muka saba, a zauren matasa na shirin yau da gobe shirin matasa inda muke zakulo maku batutuwa da suka shafi rayuwar matasa musamman da kuma al’umma gaba daya, da kuma tattaunawa akan su da nufin samo mafita da kara ilimantarwa dangane da zamantakewar al’uma.

A wannan karon akalar shirin ta waiwaya ne akan shafukan kafar sadarwa irin su facebook, da WhatsApp, Twitter da sauran su, musamman yadda jama’a ke amfani da wadannan shafuka wajan yin maganganun da suka ga dama ba kayyadewa, wato zaka rubuta ka jefa ba tare da wani y ace maka a’a ba a cikin wannan wata na Ramadana.

Akwai irin wadannan maganganu da jama’a kan yi ta wadannan shafukan da a zahiri wasu ko kudi ka basu, baza su iya yin irin ta a fili ba amma dasgike rubutawa a ke a tur aba tare da ganin ido ba jama’a sun mayar da hakan tamkar ba komi ba.

Kamar yadda kowa ya sani, wannan wata na Ramadana, wata ne da ake bukatar kowane musulmi ya tsarkake kansa domin samun albarkokin da suke cikin wannan wata mai al’farma. Ta dalilin haka ne zauren ya gayyaci Barister Maryam Ahmad Abubaka, wadda ta kware wajan amfani da irin wadannan shafuka da kuma comrade Sa’idu Dakata wanda shi kuma jami’I ne a cibiyar fasahar sadarwa da ake cema Center For Information Technology and Development. Akwai kuma malam Nura Ma’aji, dan gwagwarmaya kum kwararren malami daga jami’ar Bayero dake Kano.

Malaman sun bayyana alfanun kafafe da shafukan yanar gizo da kuma illolin da wadannan shafuka suke dasu musamman akan matasa da al’uma baki daya.

Saurari cikakkiyar hirar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG