‘Yan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich sun yi ta wallafa sakonni a shafukan zumunci na Internet a jiya lahadi, domin bayyana murnar lashe kofin gasar lig-lig ta Jamus, watau Bundesliga, a shekara ta uku a jere.
Shugaban kulob din, Karl-Heinz Rummenigge, ya bayyana ta Twitter cewa lashe kofin Bundesliga a shekara ta uku a jere wata gagarumar nasara ce.
An tabbatar da Bayern a zaman zakarun Bundesliga jiya lahadi a bayan da kungiyar da take ta biyu a teburin, Wolfsburg ta sha kashi a hannun Borussia Monchengladbach da ci 1-0, abinda ya bar Bayern a saman teburin Bundesliga da ratar maki 15 yayin da wasanni 4 kacal suka rage.
Rummenigge yace, "kare wannan kambi, gagarumar nasara ce ga kwach namu, Pep Guardiola da dukkan ‘yan wasanmu, musamman da yake akwai ‘yan wasanmu da dama da suka kasa bugawa saboda sun tafi buga gasar cin kofin duniya ma kasashensu."
Rafinha, Dante, Thiago Alcantara duk sun fito ta Twitter su na yaba wannan nasara, har ma Alcantara na cewa, jinjina ga dukkan ‘yan’uwana ‘yan Bayern. Mune zakaru!!