Shafin sada zumunci mafi farin jini a duniya yana kara yin farin jini fiye da yadda kowa ke zato.
A ranar litinin 24 Agusta, 2015, mutane har biliyan daya ne, watau miliyan dub u daya, suka hau kan Facebook a bisa cewar wanda ya kirkiro wannan shafin, Mark Zuckerberg.
Ya ce, "a ranar litinin, kashi daya cikin 7 na illahirin al'ummar duniya sun hau kan Facebook domin yin hulda da abokai da 'yan'uwansu. Idan muna maganar kudi, muna amfani da kiyasi, amma wannan abu dabam yake. Wannan shine karon farko da muka cimma wannan gacci, kuma matakin farko ne kawai na hada illahirin al'ummar duniya wuri guda."
Yawan mutanen dake amfani da Facebook a fadin duniya, ya buwayi duk sauran shafukan sada zumunci dake kan intanet. Wannan wata babbar nasara ce ga masu kula da fadada wannan shafi na Facebook, wadanda suke ci gaba da samo hanyoyin janyo ra'ayin mutane duk da cewa kasuwarsu a Amurka, inda suek da cibiya, ta kusan cika ma baki daya, kusan kowa na amfani da Facebook.
Wani yunkurin da kamfanin Facebook ke yi ta hanyar INTERNET.ORG, wanda zai rika samar da intanet ga kasashe masu tasowa ta hanyar yin amfani da jiragen sama masu amfani da hasken wutar lantarki, zai kara bunkasa ayyuka da kuma masu amfani da Facebook nan gaba.