Gyara Mana Kasa Kadai Ne Abinda Zai Hana Mu Tafiya Ci Rani Inji-Wasu Matasa

A

Bayan tallafin Euro biliyan kusan biyu da Turai tayi alkawarin baiwa kasashen afrika da nufin hana kwararar 'yan gudun hijirah, wasu matasa da wakilinmu a Lagos yayi hira dasu sun bukaci samun shugabanni masu adalci ne domin samar da aikinyi garesu kamar yarda suka shedawa wa babangida jibril a Lagos.

A hirar ta su, matasan sun bayyana cewar matsalar da ke sanadiyyar arcewa daga kasar zuwa wata kasa inda ake kyamar su sabopda launin fatar su shine rashin shugabanni masu tausayi, wadanda za su sama masu aikin yi.

Wasu daga cikin matasan da suka taba samun kansu a irin wadannan kasashe sun bayyana cewa baza su fasa yunkurin sake barin Najeriya ba tunda an manta da su. A cewar su gyaran kasa shine kawai zai magance wannan babbar matsala.

Daga karshe wani daga cikin matasan ya bayyana cewa ko yana gida a zaune idan ajalinsa ya zo mutuwa zai yi dan haka su tafiya kam ba fashi. A bu guda ne kawai zai sa su dakata, wato idan gwamnati ta samar masu da aikin yi.

Ga cikakken rahoton;