Wakar Baiwa Ce A Wuri Na

Bashir Abdullahi Mawaki

A yau mun sai zantawa da wani mawaki ne Bashir Abdullahi wato wanda kuma ake kira dan Bash, wanda ya ce tun yana makarantar firamare yake da sha’awar waka, amma bai fara rera waka ba sai bayan da ya shiga makarantar sakandare.

Yace shi a wurinsa waka baiwa ce domin a duk lokacin da yake rera ta yaka sami anashiwa tare da farin cikin jin dadin wakar da yake rerawa.

Ya kara da cewa a makarantar sakandare ne ya gane irin baiwar da Allah ya yimasa na waka wanda kuma shi ya dora akai da taimakon abokinsa Bello, wanda alokacin shi Bello, yana da studio, na na daukar waka daga nan sai tafiya ta mike.

Bashir yace burin sa shine yayi fice ta yadda za’a dama dashi a filin wake wake, da nishadantarwa da kuma ilimantarwa ta yadda jama’a zasu karo da irin baiwar da Allah yayi masa.