Abinci Da Ya Kamaci Mai Azumi

Abinci Buda Baki

A yau mun waiwaye batun dafe dafen Azumi ne wai shin wani irin abinci ne ya kamaci mai yin Azumi, yayi buda baki da shi.

Mun kuma samu zantawa da Malama Hafsat, wacce tace a wannan lokaci kamata yayi mata su yawaita yin abinci da bashi da nauyi , kuma mai ruwa ruwa domin warwarewar hanji.

Ta bayyan cewa likitoci sun yi kashedi cewa a daina yin buda baki da abun sha mai sanyi domin yakan cutar da dan Adam, wanda ta bada shawara cewa abu mai ruwa ruwa kuma mai dan dimi shi ya kama ci mai azumi domin yin buda baki.

Ta kuma shawarci mata da su dinga daidaita hannu a wajen yin girki domin a wannan zamani almajirai da yara duk suna azumi gudun zubar da abinci, maimakon samun lada