Zanga Zanga Da Korafe Korafen Iyayen Yara A Jihar Sokoto Son Zuciya Ne Kawai - Inji Alhaji Yahaya Ibrahim

Kamar yadda iyayen yara a jihar Sokoto suka yi zanga zangar lumana ta nuna kin amincewa da bada filayen da ke jikin wasu makarantu da gwamnatin jihar ta ba wasu jama’a domin gina shaguna, wasu daga cikin wadanda aka ba shagunan sun mayar da martani wajan kalubalantar korarfe korafen da iyayen suka yi.

A cewar iyayen yaran, bada filayen domin gina shaguna babbar barazana ce ga tarbiyar ‘ya’yan su, domin kuwa sun bayyana cewa makarantun jeka ka dawo ne, dan haka a cewar su kasancewar wadannan shaguna babu abinda zai haifar illa bata yaran jama’a.

Sun kara da cewa ko a yanzu haka leburorin da ke ayyukan gina shagunan sun fara tsayar da ‘yan matan suna yi masu Magana, kuma wannan na faruwa ne kafin a kammala gina shagunan. Dan haka idan aka gama lallai ba karamar illa abin zai haifar ga tarbiyyar yara mata dake makaranta a wurin ba.

A nasu bangare kuma wadanda aka ba filayen sun ce korafe korafen iyayen yaran duk na son zuciya ne kawai, Alhaji Yahaya Ibrahim Sokoto ne shugaban wadanda aka ba shagunan kuma ya yi Karin bayanin cewa korafin duk ba gaskiya a ciki, dpmin kuwa gina shagunan ne kadai zai magance irin wadannan matsaloli.

Ya kara da cewa da farko kafin a gina shaguna a kusa da makarantar Nagarta, da nan ake daukan matan aure ana lalata da su, amma daga lokacin da aka gina shagunan, gab daya masu aikata hakan suka daina zuwa wurin. Dan haka a cewar sa, gina shaguna a wurin zai kara wa makarantar da ‘yan makarantar kariya daga lalacewa ko kuma fada wa cikin irin wannan hali.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna Daga Sokoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Zanga Zanga Da Korafin Iyayen Yara A Sokoto Son Zuciya Ne Kawai Inji Alhaji Yahaya Ibrahim