Babban kwamitin Olympic ya fitar da sanarwar cewa dukkan ‘yan wasan da aka tantance na kasar Rasha zasu iya shiga wasannin da za’a gudanar na olympic wato Rio De Janeiro na kasar Brazil daga 5 zuwa 21 ga watan agustan wannan shekarar.
Kwamtin yayi wannan Magana ce saboda ‘yan wasan kasar Rasha da hukumar guje guje ta duniya ta ce bazata basu damar shiga wasannin ba saboda badakalar nan data mamaye sha’anin wasannin guje guje a kasar wanda ya shafi yin amfani da kwayoyi masu kara kuzari.
A cewar hukumar Olympic COO ta duniya, tana da shakka sosai akan ‘yan wasan kasar Rasha musamman dangane da wannan dabi’a ta amfani da kwayoyi masu kara kuzari wadda ta zama ruwan dare a kasar.
Masana sha’anin wasan kwallon kafa kuma sun ce filayen da ake amfani da su a kasar Faransa, da dama daga ciki sun nuna gajiya da rashin cika ka’idar karbar bakuncin manyan wasanni kamar irin wasannin kasashen Europe da yanzu haka yake wakana a kasar domin kuwa a cewar su, daga fashewar kwallo zuwa faduwar ‘yan wasa babu dalili ya tabbatar da hakan.
Haka-zalika a wasannin kwallon kafa na nahiyar Turai anga wani abin mamaki a wasan da aka yi tsakanin kasar Faransa da Switzerland a rukunin su, anga rigunan ‘yan wasan kasar ta Switzerland nata kekkecewa a yayin da ake gudanar da wasan wanda aka tashi babu kwallo ko guda.
Wannan lamari ya faru ne a sakamakon dadewar da kayan ‘yan wasan suka yi kafin ayi amfani da su, yanayin zafi da rashin kadawar iska yasa suka lalace kafin a yi amfani da su amma ba’a farga ba sai da wasan yayi nisa.
Saurari Cikakken Rahoton A Nan.
Your browser doesn’t support HTML5