A yau Dr Abdullahi Pakistan na masallacin Tudun Murtala ne ya bakunci Dandalinvoa inda muka zanta da shi dangane da muhimmancin taimakawa marayu a wannan wata mai alfarma na Ramadana.
Ya bayyana mana alfanu da falalar da ke tattare da taimaka marayu muslunci , inda yake jan hankali 'yan uwa musulmi da su jajirce wajen bada taimakon komai kankantarsa, ya na mai cewa wanna shine shekara na takwas da ake baiwa marayu kayayyaki da suka hada da tufafi da abinci,
Yana mai cewa harkan na faruwane da taimakon, bayin Allah da koda wane lokaci,suke amsa kira domin tallafawa marayu.
Dr. Abdullahi, ya kuma bukaci jama’a, da kada suyi kasa a guiwa wajen taimako a wannan wata mai alfarma domin kwasan garabasar lada a wuri Allah ta’ala.
Your browser doesn’t support HTML5