Kungiyar Likitoci Ta Kasa Da Kasa Ta Gano Yara 16 Da Yunwa Ta Kusa Hallakawa A Jihar Borno

A Najeriya, kungiyar likitocin nan ta kasa-da-kasa da ake kira Doctors Without Borders da turanci, tace 'yan gudun hijira da suke a wasu sansanonin 'yan gudun hijira suna fuskantar mawuyacin halin rayuwa.

Wata tawagar likitocin kungiyar da a karon farko suka samu shiga wani sansani dake Bana a jihar Barno, sun gano yara 16 da suke fuskantar matsananciyar 'yunwa data kaisu dab da mutuwa, wanda nan da nan ta mika su ga wata cibiyar jinyar wadanda 'yunwa ta yiwa katutu.

Kungiyar ta fada jiya Laraba cewa, binciken da ta gudanar ya gano cewa kashi 19 na yara 800 da suke cikin sansanin suna fama da mummunar 'yunwa mai hadarin gaske.

Kungiyar likiticin ta ci gaba da cewa ta kirga kaburbura 1,233, 480 cikin wannan adadi na yara ne, da aka binne su cikin shekarar data shige. Akalla mutane 188 ne suka mutu a sansanin galibi saboda cutar amai da gudawa da kuma 'yunwa daga 23 ga watan Mayu zuwa yau.

Akwai mutane dubu 24, cikinsu akwai yara 15,000, a wannan adadi 4,500 'yan kasa da shekaru biyar ne.