Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe Masu Tasowa Sun Shiga Jerin Masu Cin Gajiyar Mutun-Mutumi


Mutun-mutumi
Mutun-mutumi

Alamu na kara nuni da cewar nan gaba kadan mutun-mutumi “Robot” zai maye gurbin mutane a wajajen ayyuka da dama. Bama kawai a kasashen da suka cigaba ba, harma da kasashen da ke tasowa.

A kasar Philippen, wasu matasa sun samar da wani kamfani da suke ayyuka da dama, da suka hada da daukar ma’aikata na wasu kamfanoni da samar da dangantaka tsakanin kamfanoni da al'umah hanyar magana da ma’aikata wanda ake kira “customer care” a turance.

Yanzu haka kamfanin ya fara amfani da mutun-mutumi wajen gudanar da wadannan ayuyukan. Wanda hakan zai sa milliyoyin mutane rasa aikin yi. Sai dai ana ganin cewar idan mutane za suyi amfani da irin baiwar da Allah, yayi musu, wajen kara kirkirar wasu sana’o’I da wasu ba suyi ko ba’a gabatar dasu dan amfani da mutun-mutumi ba. Domin akwai wasu sana’o’I da sai mutun mai jini a jika kawai zai iya gabatar da su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG