Hukumar Kwallon Kafa Ta Najeriya Ta Fito Da Sabon Tsarin Biyan 'Yan Wasa

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta ce a cikin sabon tsarinta na yi wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da sauran kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasa garambawul, baza ta kara biyan ‘yan wasan kudin rara da hukumar ke biyan su da dallar Amurka ba.

Wannan na daya daga cikin shawarwarin da kwamitin zartaswar hukumar ya tsayar a wani zama da suka yi ranar talata a birnin Abuja.

A yayin da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Super Eagles ke cigaba da gano bakin zaren kalubalantar wasan cin kofin nahiyar Afirka da ke karatowa, tsohon kaftin din kungiyar Rufa’I, yace ya yi imanin cewa ‘yan wasan zasu taka rawar gani a wasannin, yayin da shi kuma Chief Gabriel Chukwu Gabros shugaban kungiyar FC ya bukacesu da suyi ma kansu fada domin duk abinda suka yi tamkar kansu suka yiwa.

Rahotanni daga majiya kwakkwara kamar yadda Mujallar Vanguard ta wallafa sun bayyana cewa za’a rika biyan ‘yan wasanne dangane da irin kokarin da suka tabuka wajan kowacce gasa, ba kamar yadda ake biyan kowanne dan wasa kudi dalar Amurka dubu goma a da ba.

Ya kara da cewa yanzu hukumar ce zata zauna ta tsara abinda taga ya dace ta biya ‘yan wasa bisa ga irin kwazon da bajintar da suka nuna a karshen kowacce gasa.