Kungiyoyin matasa na jam’iyyar PDP 25 ne suka nuna damuwar su a rikicin jam’iyyar da yaki ci yaki cinyewa, matakin da yasa suke ganin lokaci yayi a bangaren Ali Modu Sheriff da Ahmed Muhammad Makarfi su kai zuciya nesa domin daukar matakan ceto jam’iyyar daga halaka.
Tsohon sakataren jam’iyyar PDP a Jigawa, kuma shugaban kungiyar siyasar akida ta kasa Aliyu Muhammad Tukur Gantsa yayi tsokaci da kakkausar murya.
Ya ce “to a yau mun sami kanmu a wani hali na rigingimu da suke faruwa a wannan jam’iyya shiyasa muka taru gabadayanmu matasa masu kishin demokaradiyya, masu kishin PDP, masu kishin Najeriya, da kuma dorewarta a kasa da kuma karbabbiyar demokaradiyya.
Shiyasa muka ga cewar yakamata muyi kira ga wadannan sauran mazan jiya da suka kafa wannan jam’iyya da suzo su taimaka domin gyara matsalolin da suka dabaibaye wannan jam’iyya ta PDP”.
A wannan yanayin taronne hajiya Yalwan Shata ta ce tayi wannan jam’iyya har na tsawon shekaru 16, dan haka tana ganin yakamata manyan shugabannin kungiyar subi umurnin taron kungiyar da aka yi a Fatakwal kwana kwanan nan, domin ta haka ne kawai jam’iyyar zata iya magance matsalolinta.
Babban burin matasan dai shine domin rushe shingen dake tsakanin shugabannin biyu wato Ali Modu Sheriff da Ahmad Muhammad Makarfi.
Saurari cikakken rahoton anan.
Your browser doesn’t support HTML5