Ministan matasa da wasanni Barista Solomon Dalung ya ce ya zama wajibi matasa su rika gujewa duk abin da ka iya kawo tashin hankali idan ana bukatar wannan kasa ta cigaba.
Barista Solomon Dalung wanda ya jagoranci tawagar kiristoci domin shan ruwa a gidan Sheik Dahiru Usman Bauchi tare da al’umar musulmi ya ce dama tun farko akwai kyakkyawar alaka tsakanin musulmi da kirista, domin haka ya zama wajibi a kula da wannan kyakkyawar dandantaka.
Ministan ya ce “zan yi amfani da wannan dama domin bayyana farin ciki na musamman ganin yadda malam sheik Dahiru ya nuna mana dattako, da kauna, da karamci, ya karbemu kamar yadda ya saba. Mun ci abinci tare sa’annan kuma ya bamu shawarwari masu kyau wadanda zasu kawo zaman lafiya a tsakanin musulmai da kiristoci.
Dan haka ina rokon matasan wannan kasa tamu Najeriya da cewar su kasa kunne ga koyarwar da zata amfanesu, duk wata koyarwa da zata tada zaune tsaye to a guje mata. Domin kuwa babu littafin da ya goyi bayan tashin hankali.
Akwai dangartaka mai asali tsakanin musulmai da kiristoci tun da dadewa, kuma zamu cigaba da kiyayewa da mutumta wannan dangartaka da goyon bayan juna domin a gina kasa”.
Shima Sheika Dahiru wanda aka sha ruwa a gidan sa, ya bayyana yadda yaji dadin wannan ziyara, ya kuma yi bayani mai ban shi’awa da kuma kara jadda yadda dangartakar take tsakanin mabiya addinan biyu da kuma muhimmancin ta.
Latsa nan domin sauraren cikakkiyar hirar.
Your browser doesn’t support HTML5