A yau bakuncin Abdulwahab Awarwasa muka samu , furodusa, kuma DJ, a masana'antar Kannywood, mai komai da ruwanka ya ce yana jin dadin sana'arsa.
Ya ce ya fara harkar fina finai kimani shekaru goma sha biyu da suka wuce kuma duk abin da ake nema dai dai gwargado Allah ya cika masa burinsa koda yake ya ce dan Adam ya mutuwa da buri.
Awarwasa ya kara da cewa idan dake harka ta sauti ne a kannywood toh shi kam Alhamdulillahi, sai godiya.
Ya kara da cewa Allah ya taimake shi a kannywood dalilin Ali Nuhu, wanda shine jagoran sa a masana'antar kannywood.
A wasu lokutan ma har kayan tande-tande da lashe lashe ya kan kai wurare da ake daukar fina-finai domin ya sayar duk a wani yunkurin samawa kansa kudaden shiga.
Your browser doesn’t support HTML5