WASHINGTON D.C —
Asusun bada lamuni na duniya IMF, da sauran ma’aikatun kudi da masana tattalin arziki sun bayyana karyewar darajar Naira a matsayin lamarin da kasar zata ci ribarsa zuwa nan gaba.
Sun bayyana cewa sun yi imanin cewa manufofin sabuwar gwamnatin mai ci yanzu zasu habaka tattalin arzikin kasar, da kuma samar da ci gaba mai dorewa da samar da guraben ayyuka da kuma rage dogaro ga danyen man fetur da kasar ke yi, ta hanyar samar da hanyoyin samun ayyuna yi iri daban daban.
Bayanan sun kara da cewa karyewar darajar Nairar zata samar da yanayi da zai dauki hankalin masu zuba hannun jari da zasu gina matatun mai wanda zai ja hankalin ‘yan kasuwa su rika shigo da mai daga kasashen waje.