Mai Ake Ciki Game Da Kamun Matashin Dan Jarida Salkida

Shalkawatar tsaron Najeriya ta ce bata da masaniya akan kama matashin dan jaridar nan mai suna Salkida, wanda rundunar sojin Kasar ta saka sunansa a jerin sunayen wadanda take nema ruwa a jallo bisa zarginsa da alaka da kungiyar Boko Haram.

Mai Magana da yawun sojin Najeriya Birgediya Janar Abubakar ne ya tabbatarwa da mujallar Daily Trust hakan.

An kama matashin dan jaridar ne ranar litini data gabata a filin saukar jiragen sama ta kasa da kasa dake birnin tarayya Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke Salkida ne a kofar jirgin sama na Emirates Flight, daya kawo shi birnin Abuja.

Rundunar sojan Najeriya ta saka sunan Salkida tare da wasu mutane biyu a cikin jerin sunyen wadanda take nema ruwa a jallo bayan wani sabon bidiyo na daliban makarantar Chibok sama da dari biyu da ‘yan kungiyar Boko haram suka sace.