Taya Ake Gane Cutar Nimoniya, Kafin Ta Hallaka Mutun?

Zuciyar Dan'adam

A lokutta da yawa mutane kan zauna da wasu cututtuka, batare da sun san abubuwan da suka haddasa musu cutar ba, da kuma daukar matakin da suka kamata don magance cutar. Bincike ya bayyanar da nau’o’in cutar “Pneumonia” wadda akafi sani da Nimoniya, wata cutace da mutane kan dauke ta a dalilin aikata wasu abubuwa.

Nau’i na farko shine “Bacteria Pneumonia” itace nau’i da akan sameta a jikin kowa, babu babba babu yaro, akan kamu da ita ne a sanadiyar wasu cututtuka da sukan shiga cikin jikin mutun, ta hanyar kura, kusantar waje da bashi da tsafta, haka idan mutun na dauke da mura takan rikide ta koma cutar nimoniya idan ba'a dauki mataki cikin gaggawa ba.

Ta biyu kuwa itace “Mycoplasma Pneumonia” itace cutar nimomiya da akafi samun ta a jikin yara kanana da matasa, a sanadiyar wasan ruwa, ko kusantar wuri mai danshi, ko wasa a wajen da ba iska nagartacciya. Zama cikin daki mai dauke da zafi, ko inda mutane su kayi yawa, duk suna haddasa wannan nau’in na nimoniya.

Ta uku kuwa itace “Viral Pneumonia” tana samuwa ne a sanadiyar yadda mutane, kanyi mu’amala da masu dauke da cutar, wanda takan fara a matakin farko sannu a hankali, sai ta kai wani matakin da maganin ta na iya zama da wuya.

Akwai wasu da dama a cikin jerin cutar nimomiya, da ya kamata ace mutane su yi kokarin gujema, musamman wajen samun yanayi mai inganci.