A ranar Laraba da ta gabata ne, fittaccen dan wasan kwallon rami nan “Golf” Tiger Woods, ya bayyanar da dawowar shi filin wasa. Tun a ‘yan kwanakin baya ne mutane keta rade-radin cewar, dan wasan ya gama zamanin shi, ganin cewar ya kwashe tsawon shekaru biyu bai buga wasaba.
Duk dai da cewar, anyi ma dan wasan aiki a gadon bayan shi sau uku, yanzu haka dai ya shirya ma buga wasanni uku, wasan kamfani Safeway, da na kamfanin jiragen sama na kasar Turkish, sai wasan da za’a gabatar a Bahamas.
Rade-radin cewar bazai sake buga wasa, yazo ne a dalilin rashin buga wasan shi tun daga shekarar 2014, hakan yasa ya sauka daga matsayin shi na shahararre zuwa mataki na kasa.
Abun tambaya a nan shine, wai idan har dan wasan ya dawo wasa, zai iya wani tasiri kuwa? Dan wasan dai ya kafa tarihi a fadin duniyar kwallon “Golf” wanda ya lashe wasnnin goma sha hudu.