Dabbobi Sun Sa Malaman Yanayi Azumin Sati 2 Ba Abinci Ba Ruwa!

Dabbar Polar Bear

Tawagar masu binciken yanayin duniya “Meteorologists” na kasar Rasha, su biyar 5, sun yi azumin boyo a cikin dusar kankara na sati biyu. Hakan ya faru ne a sanadiyar shiga cikin wani tarko da su kayi na dabbar da ake kira “Polar Bear”

Sun dai makale ne a cikin wani dan karamin daki, a kauyen “Izvestiy TSIK Island” wanda ke da tazarar kimanin kilomita dubu biyu da dari takwas 2,800 daga babban birnin Moscow. Ma’ikatan dai sun makale ne, bayan karewar wani sinadari da suke amfani da shi wajen tsoratar da babbobin, daga nan sai dabbar bear suka fara cinye karnukan da suka kai ma’aikatan cikin tsaunin.

Bisa ga al’ada a duk kasar dake fama da matsananciyar dusar kankara, akanyi amfani da karnuka ne wajen tafiye-tafiye, don mota ko mashin basu iya tafiya akan dusar kankara.

Hukumomi sun shiga cikin halin tsoro, na yadda mutanen suka kwashe tsawon kwanaki babu labarin halin da suke ciki, kodai da aka isa wajen su a tekun Kara, dake cikin kungurmin daji, don kai musu agaji, an tarar da dabbar bear sunyi musu kawanya, amma dai a karshe an samu nasarar cetosu.