Wani dalibi a jami’ar Ilorin, jihar Kwara ya bukaci hukumar makarantar ta dakatar da shi daga karatu a jami’ar inda ya bayyana cewa yayi satar amsa a lokacin da ya yake rubuta jarawar kammala karatun sakandire wato WAEC.
Dalibin wanda yake mataki na uku na kammala karatun sa na jami’a a fannin zamantakewa da halayyar dan’adam mai suna Abolarin ya bayyana cewa baya bukatar ci gaba da karatu tunda bai nemi takardun kammala sakandire ta hanyar data dace ba, a cewarsa shi kiristan kwarai ne dan haka bazai ci gaba da amfani da haramtaccen sakamakon jarabawa.
Mujallar Daily post ta wallafa cewa mahukuntan jami’ar sun bayyana cewa sun amince da takardar dakatar dashi daga karatun kamar yadda ya bukata.
Dalibin ya mikawa hukumar makarantar takardar neman dakatar da karutun nasa ne ta ofishin mataimakiyar shugabar jami’ar, inda ya rubuta cewa bai dace ya ci gaba da karatu akan takardun da suka samo asali ta harantacciyar hanya, wato satar amsa yayi a lokacin da ya zana jarabawar.
Dan haka ya nemi a dakatar da shi domin a cewar sa, zai sake komawa ya fara karatun neman takardar ta halliyar hanya tun daga farko. Mataimakin babban daraktan jami’ar ya bada tabbcin dakatar da dalibin daga karatu a jami’ar kamar yadda ya bukaci a yi masa.