Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu Mata Uku Da Ake Zargi Da Shirin Kai Harin Bam A Faransa


‘Yansandan Faransa sun kama wasu mata uku da ake musu zaton suna yunkurin shirya kai hari, mai nasaba da wata mota da aka gani a wannan makon dauke da silindar gas guda shida a birnin Paris.

Ministan harkokin cikin gida na Faransa, Bernard Cazenueve yace wa’ayannan mata uku masu shekaru daga 19 zuwa 39 mata ne da aka sauyawa raa’yin akida da suke da niyar daukar wasu matakan kawo mummunan tashin hankali a kasar.

Kama su ya biyo bayan wani bincike ne da aka gudanar akan wata mota da a kama da silindar gas a kusa da cocin Notre Dame dake birnin Paris afarko farkon wannan mako. Mai motar mahaifin daya daga cikin wadanda ake zargin ne.

An harbe daya daga cikin matan, amma kuma wani dan sanda ya samu raunin sukar da aka yi mishi da wuka.

Daga farkon shekarar 2015 zuwa yanzu, sama da mutane dari biyu ne aka kashe a Faransa a hare haren ta’addanci. A wannan shekara kadai, mutane 260 aka kama a Faransa masu nasaba da harkokin ta’addaci, inji Cazeneuve.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG