Akwai Bukatar Sa Hannun Malamai A Harkokin Film Domin Tsabtace Masana'antar

A shirinmu na nishadi yau muna tare da Naziru Auwal ne wanda aka fi sani da Dan Hajiya, furudosa kuma daraktan fina-finai a kannywood industry wanda ya shafe shekaru biyar a harkar.

Ya ce Jamila Nagudu na daya daga cikin wadanda suka jawo shi harkar fim bayan ya kammala diplomarsa a lokacin da yake zaman jiran sakamakon jarabawarsa, gudun kada yayi zaman banza sai ta janyo shi harkar fim.

Ya kara da cewa sana'ar fim sana'a ce ta dogaro da kai tare da jan hankalin malamai da su shigo harkar domin tsabtace masana’antar.

A fanninmu na tsegumi kuwa fitattaciyar jarumar Nollywood Cossy Orjiakor ta kalubalenci ‘yan sanda da idan sun isa su zo su kamata bayan ta sanyawa magunanta suna Buhari da Jonathan.

Ta bayyana haka ne a shafinta na Instagram a ranar juma’ar da ta gabata, tare da bayyana irin dan sanda da zai iya kamata.

Fitattacen mawakin nan na hip-hop dan kasar Africa ta kudu, Mduduzi Edmund Tshabalala wanda aka fi sani da Mandoza ya mutu yana da shekaru 38 da haihuwa.

Mawakin dai ya sha fama da cutar cancer wato sankarar kwakwalwa shekaru biyu da suka wuce.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Bukatar Sa Hannun Malamai A Harkokin Film Domin Tsabtace Masana'antar