Mohamed Imran suleman wanda aka fi sani da big gentle ya ce ya fara wakar Hausa hip hop wato waka mai kama da zaurance ne domin kawo canji ga salon waka, domin su yi gogaiya da mawaka a fadin duniya tare da baiwa matasa damar mayar da hankalinsu ga nasu mawakansu na gida.
Big gentle ya ce waka ta zama kamar dabi’arsa, wanda ya ce hip-hop raps ko ba murya idan mutun yana kallo a akwatin talabijn zai fahimci kadan daga cikin abinda suke fada, ko da yake ya ce akwai bambanci tsakanin hip-hop da sauran mawaka, wajen salo .
Mawakin ya kara da cewa shekaru biyar da suka wuce ya fara wakar hip- hop kuma ya fara ne sanadiyar gasar waka , kuma ya aminta da cewar waka wata hanya ce ta tura sakonni ga al’umomi.
A fannin tsegumi kuwa fitattacen dan wasan barkwancin nan Bovi ya ce shekaru 20 bayan mutuwar 2pac har kawo yanzu akwai wasu darussan marigayin da yake amfani da su, ya kara da cewa har yanzu wakokin da yayi na tasiri ga alumma haka zalika yake so wassaninsa na raha su amfani mutane ta wasu hanyoyin .
Daaga karshe ya kara da cewa a halin da ake ciki a yanzu mutane sun fi rajja’a ga abin duniya da kyalekyalen zamani.
Saurari rahoton Baraka Bashir domin karin bayani.