Facebook Ya Hade Manhajar Instagram Da Messenger Wuri Guda

Facebook yace ya kirkiri wata sabuwar manhajar app da zata taimakawa ‘yan kasuwa wajen hade shafunansu na Facebook da Messenger da kuma Instagram guri daya.

Kamfanin Facebook dai na kokarin taimakawa masu gudanar da kasuwanci ta kafafen sadarwa su rika bibiyar kwastomominsu ta yanar gizo.

A yau Alhamis ne Facebook yace masu kamfanoni zasu iya hade shafunansu guri guda, ta yadda zasu samu saukin ganin yadda kwastomominsu ke mu’amula a shafunan sadarwa guda uku na kamfanin lokaci daya.

Yanzu haka duk kamfanin da yake amfani da wannan sabuwar fasaha zai samu kundin ayije sakonni guda daya, wadda duk sakonnin da aka tura masa daga shafunan uku zai iya gani.

Haka kuma kamfanin zai iya ganin duk wani sharhi ko tambaya da mutane suka kafe, ta yadda kamfanin zai iya rubuta amsa akan lokaci ba tare da bata lokaci ba.

Masu kamfanoni zasu iya sauke wannan manhaja ta kan wayoyinsu domin fara amfani da ita cikin gaggawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Facebook Ya Hade Manhajojin Instagram Da Messenger Wuri Guda