Frank Lampard Ya Yi Bankwana Da Kwallon Kafa

Tsohon dan wasan kwallon kafa na kasar Ingila Frank Lampard ya ajiye takalmansa na taka leda, Lampard mai shekaru talatin da takwas da haihuwa kafin ritayarsa ya buga wasanni a kungiyoyin kwallon kafa daban daban a duniya wanda suka hada da Kungiyar Westham united, Chelsea, Manchester City, dukkansu a kasar Ingila.

Daga bisani ya koma Kungiyar kwallon kafa ta MLS, dake Newyork City, a Kasar Amurka ya kammala kwantirakinsa a MLS, a shekara 2016.

Frank yasamu nasarar lashe manya manyan kofuna har guda goma sha daya duka a kungiyar ta Chelsea, inda ya lashe firimiya lig ta kasar Ingila sau uku, FA Cup Sau hudu, EPL, Sau biyu sauran kofunan sun hada da Championship League, guda daya kofin zakarun Turai UCL, Sau daya ya kuma shafe shekaru Goma Sha ukku a kungiyar Chelsea.

Lampard ya wakilci kasarsa ta Ingila, a wasanni sama da dari

inda ya shafe shekaru ashirin da daya yana fafatawa a fagen tamola.

A bangaren wasannin firimiya lig da akeyi a kasar Ingila ta shekarar 2016/2017, Gobe za'a shiga mako na ashirin da hudu

Mai rike da teburin Chelsea, zata kece raini da Arsenal, Hull City zata karbi bakuncin Liverpool, Everton da AFC Bournemouth, Crystal palace da Sunderland.

Ita kuwa Westbromwich, zata gwabza ne da Stoke City, Wartfotd su barje gumi da Burnley, Southampton zata kece raini da MiddleBrough.