An Danke Lucas Hernandez Bisa Zargin Cin Zarafin Budurwar Sa

Jami’an tsaro a kasar Spaniya sun cafke dan wasan klub din Atletico Madrid, Lucas Hernandez, bisa zarginsa da cin zarafin budurwarsa, ‘yan sandan kasar Spain sun tabbatar wa mujallar GOAL.

An kama dan wasan mai shekara 20 da haihuwa, ranar juma’a da misalign karfe 2:30am, bayan an kwantar da budurwar a asibiti, duk da dai raunikan da taji ba wasu na tada hankali bane.

Ana sa ran gurfanar da Hernandez, wanda ke bugawa kungiyar kwallon kafa masu kasa da shekaru 21 wasa ta kasar Faransa, a kotun Majadahonda, wani kauye dake Arewa da Madrid a ranar Jumu’a, bisa zargin cin zali na jinsi.

Rahotanni daga kasar Spain, sun nuna cewa ita budurwar tasa bata kai kara ba saboda tana jiran ta gana da lauyan ta.

Idan Alkali mai shari’ar yaga cewa babban laifi ne dan wasa ya aikata, za’a cigaba tuhumarsa lamarin da zai iya sandiyar dakatar dashi daga wasa.

Hernandez dai yayi ma kulob din Atlentico, wasa sau 11 a wannan kakar wasannin, bayan yayi ma kulub din capital na copa del ray, wanda suka yi da L’Hospitalet, a shekarar Disambar shekara ta 2014.

Dan uwansa, Theo na left-back yana cikin klub din vicente calderon, Amma yanzu an bada aron shi a Alaves.

Klub din Atletico Madrid, dai basu ce komai ba Game da lamarin.