Shahararren dan wasan danben Boxing ‘Lawrence Okolie’ wanda ya shahara a wasannin zakaran Rio Olympics 2016. Ya lashe wasan shi da suka gwabza, inda yayi nasara cikin sakon ashirin 20.
Dan wasan danben mai shekaru ashirin da hudu 24, dan asalin kasar Najeriya, amma haihuwar kasar Birtaniya, ya kara da dan wasa Geoffrey Cave. Ya gwabje shi da nushi biyu da hannun hagu, hakan yabashi damar lashe wasan.
Wannan wata karin damace da ya samu, biyo bayan doke dan wasa Anthony Crolla, da yayi a fillin wasan danbe na garin Manchester, a kasar Birtaniya. Dan danben dai ya rubuta a shafin shina tweeter cewar, “Abun da ban mamaki, wannan nasarar cikin sakon ashirin 20, na dawo da karfi na”
Yace babban abun da ya bashi sha’awar shiga wasan danben boxing, shine yadda yake kallon wasan, a lokacin da yake aiki a gidan abinci na McDonald. Yana ganin irin yadda ‘yan wasan ke bashi sha’awa. Yanzu haka gashi yana neman zama zakaran gwajin dafi a fagen danben boxing.