Lionel Messi, Na Shawarar Barin Barcelona A Watan Mayu.

Dan Wasa Lionel Messi

Ana sa tsammanin shahararren dan wasan kwallon kafar kungiyar Barcelona, Lionel Messi, zai sabunta kwantirakin shi da kungiyar ta Barcelona. A watan Mayu idan Allah ya kai rai, wanda ake sa ran zai cigaba da zama a sansanin horas da ‘yan wasa na kungiyar dake Capm Nou har zuwa shekarar 2022.

Kwantirakin dan wasan dai a klob din zata kare a karshen kakar 2018, akwai rade radin cewar dan wasan mai shekaru 29, zai canza sheka zuwa wata kungiyar.

Dan wasan dai ya kwashe duk ilahirin tsawon shekarun wasan shi, a kungiyar ta Barcelona, a cewar gidan radiyon Spanish Cadena, mahaifin dan wasan da manajan shi Messi Mr. Jorge, zasu cinma matsaya dangane da zaman shi a kungiyar, ko kuma komawa wata kungiya daga nan zuwa watan Mayu.

Ana dai sa ran sabuwar kwantirakin ta zama ta shekaru 5, har zuwa shekarar 2022, dai-dai lokacin da dan wasan zai cika shekaru 35 da haihuwa. Ya fara wasan kwallon shi ne a shekarar 2004. Dan wasan ya lashe manya manyan kofufuka 29, inda kuma aka bayyanar da shi a matsayin dan wasa da yafi kowa a duniya har sau 5.