A kasashe da suka cigaba, karya dokar tuki kwara daya na iya jefa mutun cikin babbar matsala. Wani mutun a garin Vancouver ta kasar Canada, wanda yayi wani abun ban mamaki, a lokacin da ya dauki wayar shi da kwamfutar hannu, ya daure su akan sitiyarin motar shi.
A iya tunanin shi, mafi akasarin mutane na tuki suna amfani da na’ura daya ne, amma shi yana ganin bari yayi amfani da guda biyu, kana ya daure su akan sitiyari.
A dai-dai lokacin da yake tafiya, Dan-sanda mai kula da hanya, ya tsaida shi, inda ya ganshi da na’urorin biyu, an tambaye shi dalilin shi na yin hakan, wanda bai bada wani dalili mai karfi ba.
An kuma tambaye shi ko yasan da cewar yin hakan ya saba dokar titi? Ya amasa duk tuhumar da aka yi mishi, kana an ci shi tara ta dallar Amurka sittin da biyu $62 kwatankwacin naira dubu ashirin da biyu.
Ofishin ‘yan sanda na garin, sun wallafa wannan labarin da hotunan motar mutu min a shafin su, don ilmantar da mutane akan hadarin tuki da kuma amfani da waya ko wani abu da ka iya daukar hankalin mutun.