Kamfanin Apple Na Tursasama Jama'a Siyan Sababbin Wayoyi

Kamfanin Apple na kokarin kare kan shi, daga zargin da ake mishi, na aikama ma’abota amfani da wayoyin iPhone, wani link da niyyar sabutan manhaja, wanda sabuwar manhajar take sa waya aiki kadan-kadan.

Wasu mutane dake amfani da wayoyin iphone ne suka shigar da kamfanin kara, an bayyanar da dalilin kamfanin Apple nayin hakan, da cewar suna bukatar mutane masu amfani da tsofaffin wayoyin iPhone da su siya sababbin wayoyi.

Mutane daga jihohin Illinois, Ohio, Indiana, da Carolina ta Arewa, sun shigar da karar kamfanin, kuma sun shaida cewar babu wani dalili da zai sake sasu siyan wayar apple.

Zargin dai na kunshe cikin takardun da aka gabatar ma kotun tarayya a birnin Chicago, haka wasu ma da dama sun gabatar da irin wannan karar a gaban kotu a wasu sauran jihohin kasar Amurka.

Kamfanin dai na Apple, ya karyata wannan zargin, da cewar babu gaskiya a kan wannan maganar, kuma kamfanin na kokarin inganta wayoyin shi. Wanda hakan yasa suke sabutan na’urorin tsofaffin wayoyi.