Za'a Sake Harba Rokar "Elon Musk SpaceX" Zuwa Duniyar Wata

Hukumar “Elon Musk SpaceX” hukuma ce da ke kula da shawagin jiragen sama na “Rocket” a sararrin samaniya. Yanzu haka dai hukumar sun kammala shirye-shiryen su don gabatar da sabon jirgi da suka kirkira don zuwa sararrin sama jannati.

A ‘yan kwanakin baya ne, daya daga cikin rokokin shiga sararin samaniya ya kama da wuta, a dai-dai lokacin da suke kokarin zuwa duniyar wata. Hukumar ta SpaceX zasu kaddamar da roket mai suna Falcon-9, daga jihar California. Wanda ake sa ran zai tafi shawagi cikin sararrin.

An dai kwashe tsawon lokaci wanda babu wani jirgi da ya shiga duniyar wata, biyo bayan kamawa da wuta da daya daga cikin jiragen roket da yayi, a wani yunkurin tashi da yayi.

Hakan yasa anyi asarar jirgin roket da aka kiyasta kudin shi, zai kai kimanin dallar Amurka milliyan sittin da biyu $62M. Kamfanin SpaceX dai mallakar kamfanin Tesla Motors ne. Daya daga cikin matuka jirgin roket din dai ya tsira da ran shi.