Abin Takaici Ne Ganin Matasa Na Zaman Kashe Wando

Ummul khairi Suleman

Ta ce na fara sana’ar hallaka-kwabo tun ina makarantar firamare, kasancewar na taso gidanmu na tarar maza da mata na sana’a inji Ummul khairi Suleman matashiya mai aikin ofis da kuma sana’ar hannu.

Ummul Khairi na sana’ar sayar da hajja, kayan wayoyi da sauransu , inda take kokawa ga yadda take ganin wasu mata har da maza suna zauna gari banza ba tare da wata sana’ar dogaro da kai ba.

Umma ta ce tana aikin ofis sannan tana wata sana’ar domin kashe kananan bukatu, mussamam ma ganin cewar albashi baya kashe bukatun yau da gobe.

Ta fara da karamar sana’ar hallaka-kwabo, wani abu da yara kanan ke ci kana ta fara kiwon kaji da ribar data samu wanda a yanzu take sayar da hajja da duk abinda ya sauwaka.

Sai dai kamar yadda lamarin rayuwa yak e cike da kalubale, matashiyar ta ce babban kalubalen da ke ciwa masu kananan san’oi tuwo a kwarya bai wuce yadda ake karbar bashi ake kuma kin biyan kudin akan kari ba ta kara da cewa da sana’a da aikin ofis ko na gwamantin na da matukar alfanu a wannan zamani da ake ciki.

Your browser doesn’t support HTML5

Abin Takaici Ne Ganin Matasa Na Zaman Kashe Wando