Amfani Da Facebook Wajen Kama Masu Laifi

A page from the Facebook website is seen in Singapore May 11, 2011. Facebook users' personal information could have been accidentally leaked to third parties, in particular advertisers, over the past few years, according to Symantec Corp's official web bl

A ranar Asabar aka kama wani mutum, wanda ya aikata laifi, daya gudu daga jihar Idaho, bayan da ya gaiyaci abokanan sa a shafinsa na Facebook zuwa wasan horo da zaiyi a garin Boise.

Wani gidan talabijin na garin Boise yace jami’an ‘yan sandan garin Caldwell ne yaje filin wasan, bayan da suka ga gayyatar wannan mai laifin da ake nema, suka kuma kama matashin mai suna Joey Patterson ‘dan shekaru ashirin da biyu da haihuwa.

Ana dai neman wannan matashi da laifin ketta ka’idar hukuncin gyara halinka, wanda aka yanke masa hukunci bayan da ya aikata laifin zamba a baya. Yanzu haka an tsare shi a kurkuku, ba tare da bashi damar ayi belin sa ba.

Jami’in ‘yan sandan wannan yanki na Caldwell, Joey Hoadley yace galibi ‘yan sanda na amfani da shafuna sadarwa domin bin diddigin masu laifi. Inda yace “ko da masu lefi da ake nema kan wani laifi da suka aikata, ba su iya kauracewa sa bayanai shafin Facebook na su, kuma hakan na kaiwa har ga kamasu.”