Aminu Musa wanda yake zaman koch din kungiyar Giwa FC, ya bar aikin sa daga kungiyar. Tsohon mai horas da mai tsaron ragar kungiyar ta Giwa FC yayi murabus ne watanni kadan bayan aka maye Tony Bolus a matsayin mai kula da harkokin kungiyar.
Bayan yin murabus din nasa ne dai yace, “ina mai godiya ga kungiyar Giwa FC da mutanen jihar Plateau, kan damar da suka bani na yin aiki a wannan kungiya da take da guri na musammam a zuciya ta, ina mai musu fatan alkhairi ga duk abubuwan da zasuyi nan gaba.”
Rahotanni da dama na nunin cewa, Musa dai ya bar aikin sa ne a dalilin matshin lamba da yake fuskanta, biyo bayan shan kashi da sukayi a hannun Taraba FC da ci ‘daya mai ban haushi, a wasannin premier da akeyi.
A yanzu haka dai kungiyar na matsayi na biyar kan teburin wasannin na premier League, kuma suna da maki 46 da suka samu cikin wasanni 29 da suka buga.