Amurka Zata Taimakawa Najeriya Kan Daliban Chibok In Ji Kerry - 3/5/2014

Sakataren harkokin waje John Kerry, yana ganawa da shugaban hukumar bincike ta Tarayyar Afirka kan Sudan ta Kudu, tsohon shugaba Olusegun Obasanjo na Najeriya jumma'a a Addis Ababa

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya bayyana satar daliban da aka yi a Chibok a zaman mummunan laifi na rashin imani ko kan gado. Sakatare Kerry yace Amurka zata yi duk abinda zata iya domin tallafawa gwamnatin Najeriya wajen maido da wadannan ‘yanmata zuwa gidajen iyayensu.

Har ila yau sakatare Kerry yace Amurka zata taimaka ma Najeriya wajen hukumta wadanda suka aikata wannan laifin. Kungiyar Boko Haram dai ba ta fito ta dauki alhakin kai wannan harin ba.

A majalisar dattijan Amurka, sanatoci da yawa sun gabatar da kudurin yin Allah wadarai da satar daliban, tare da bayyana goyon baya ga al’ummar Najeriya. Sanatocin da suka hada da Barbara Boxer sun nemi rassan gwamnatin Amurka da su taimakawa Najeriya wajen kwato wadannan ‘yan mata.

Your browser doesn’t support HTML5

Kwato Daliban Chibok - Amurka Zata Taimaka In Ji Kerry - 0'55"