An Bukaci Hukmar JAMB Ta Kara Wa'adin Sakamakon Jarabawa

Jiya talata ne majalisar dattijai ta Najeriya ta umurci hukumar tsara jarawar share fagen shiga jami'a ta kasa JAMB da ta kara wa'adin sakamakon jarawar zuwa shekaru uku.

Kuma hakan na faruwa ne kamar yadda aka ba hukumar gargadin ccewa ta kaurace wa ba dalibai zabin makarantar da basu su ka zaba da kan su ba, kamar yadda hakan ya saba ma dokokin hukumar.

Daga yanzu dai ana sa ran sakamakon jarabawar daliban zata kai wa'adin tsawon shekaru uku.

Majalisar da umurnin ya fito wadda aka yi wa lakabi da "Sabuwar Dokar JAMB" ta sami daukar dawainiya daga Sanata Joshua Lidani dan jam'iyyar APC daga Gombe Sourth, ta bukaci hukumar tsara jarabawar da ta hada hannu da kungiyar iyayen yara, da kungiyar malaman jami'a ASSU domin samun kyakkyawan tsarin samar da kafar shiga jami'a da ta dace.

An kuma bukaci kwamitin ilimi da ya binciki lamurran da ke tattare da hukumar wadanda suka hada da zargin masu uwa a murhun da ke cin moriyar hukumar a boye.