An Fitar Da Wayoyin iPhone 7 Da iPhone 7 Plus A Kasuwa

wayar iPhone 7

Jiya Laraba ne kamfanin Apple ya fitar da wasu sabbin wayoyin iPhone har guda biyu, a wani yunkuri da yake na ganin ya janyo hankulan jama’a domin samun hanayar mamaye kasuwar waya a duniya.

Wayoyin biyu da ya fitar sune iPhone 7 da iPhone 7 Plus, baki dayansu suna dauke da fasali masu yawa ciki harda wata kamarar daukan hoto mai dauke da wata sabuwar fasaha, haka kuma suna dauke da fasahar da ko sun fada ruwa babu abin da zai same su, da dai sauransu.

Abu guda da aka canza kuma ake ganin ka iya batawa masu amfani da wayoyin iPhone rai shine rashin gurin saka na’urar sauraro wadda ake makalawa a kunne wato headphone, sai dai ayi amfani da fasahar wireless wajen sauraro ta kunne.

Cire gurin saka wayar abin saurari da kamafanin Apple ya yi a sabbin wayoyinsa na iPhone na nunin cewa masu wayoyin iPhone zasu fara amfani da abin sauraron da ake makalawa a kunne wato headphone wadda bata da waya jikinta.

Duk kuwa da faduwar kasuwar wayar iPhone a duniya, Apple yayi imanin dakatar da fitar da kayansa kasuwa har na tsawon shekaru biyu, ma’ana shine ba zai fitar da wani muhimmin abu ba har sai shekara ta 2017.

Your browser doesn’t support HTML5

An Fitar Da Wayoyin iPhone 7 Da iPhone 7 Plus A Kasuwa - 1'12"