WASHINGTON, DC —
Yankin Ozoro dake cikin jahar Delta, a Najeriya, na zaman makoki bayan mutuwar wani dan makarantar Polytechnic din jahar ta Delta.
Dalibin da aka kashe wanda ke karatun harkar kasuwanci an harbe shine a wuya a lokaci da yake barci a dakinsa dake cikin harabar makaratar.
Da take tabbatar da afkuwa lamarin kakakin rundunar 'yan Sandan jahar ta Delta Celestina Kalu, ta ce kisan nada nasaba da kungiyar asiri, kuma an samu bindiga a gefen gawarsa.
Ta kara da cewa rundunar na ci gaba da bincike akan mutuwa wannan dalibin na makarantar Polytechnic.