An Kama Tsohon Mataimakin Hukuma FIFA Da Karbar Cin Hancin Dala Dubu 50

Rahotanni da dumiduminsu sun bayyana cewa ana zargin tsohon mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Mr Eugenio Figueredo da karbar cinhancin zunzurutun kudi har dalar Amurka dubu hamsin daga wasu kanfanonin dake sayar da kayan wassanni.

Tsohon shugaban mai shekaru 83 na daya daga manyan shugabannin hukumar FIFA bakwai, kumna an cafke shi a otal din Luxury dake birnin Zurich a watan Mayun da ya gabata da zargin amsar makudan kudade a kowanne wata daga kamfanoni biyu domin tabbatar masu da basu damar cigaba da kasancewa a yawancin wasannin da za a buga a kudancin Amurka a cewar bayanan da wata kotu ta fitar daga Uruguay.

Figuereto wanda aka fara yiwa shari’a satin da ya gabata na fuskantar caje caje dake da nasaba da zamba cikin aminci da kuma yin sama da fadi akan wasu kudade ba bisa ka’ida ba, kuma a yanzu haka ana cigaba da tsare shi a gidan yari har sai an gama shari’ar.

A cigaba da bayani kan lamarin, mai shari’ar kotun ya bayyana cewa rahotanni sun nuna cewa Figueredo na amsar albashin kudi dalar Amurka dubu 40 a matsayinsa na shugaban hukumar kwallon kafa na kudancin Amurka, kuma yana amsar dalar Amurka dubu 50 a kowane wata na cin hanci inda ya zuba jari a wani kamfanin gine gine a Uruguay.