An Kama Wata Likita Na Yi Wa 'Yan Mata Kaciya A Amurka

An kama wata mace, likita a Amurka wacce ake zargin ta da yiwa yara kananan ýan mata ‘yan tsakanin shekaru shida zuwa takwas kaciya, a shari’ar farko tun kafa dokar haramta wannan ta’asa a shekarar 1996.

Jumana Nagarwala, likita ce ‘yar shekaru 44 a Asibitin birnin Detroit, dake jihar Michigan, an same ta da laifin yiwa yara mata kanana kaciya tun kusan shekarar 2005, kamar yadda mai gabatar da karar kan manyan laifuka ya bada bayani a jiya Alhamis.

Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, tace matar ta aikata mummunan laifi akan wadanda bazasu iya kare kansu ba.”

An gabatar da Nagarwala, a gaban kuliya a kotun yankin Detroit, a jiya Alhamis inda aka bada umarnin kulleta sai ranar Litinin, domin cigaba da sauraron shari’ar da kuma irin laifukan da ake zarginta dasu, wandanda suka hada da yi wa yara kanana mata ‘yan shekaru Bakwai kaciya a watan Fabrairu.