Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malala Yousafzai: An Karramata Da Lambar Yabo, Na Magajiyar Zaman Lafiya


Matashiya Malala Yousafzai
Matashiya Malala Yousafzai

Majalisar Dinkin Duniya, ta karrama matashiyar nan da ta lashe kyautar lambar karramawa ta duniya, “Nobel laureate” a turance. Malala Yousafzai.

A yayin mika mata wannan kyautar a farfajiyar shelkwatar Majalisar Dinkin Duniyar, dake New York kasar Amurka. Sakataren Janaral Antonio Guterres, ya gabatar da jawabin barka da zuwa, ga matashiyar mai shekaru 19.

A jawabin shi da yace "A matsayina na tsohon farfesa, ina cike da bakinciki, ganin yadda nake girmama daliba, mai kananan shekaru, hasalima ba wai zamanta daliba ba, zamanta yarinya mai rajin kare hakkin yara a fadin duniya’ a lokacin kuruciya ta ban samu karramawa irin nata ba.

A yayin da yake karanta jawaban da aka rubuta a cikin kyautar karramawa, da aka bata. Ya bayyana irin gudunmawar ta a duniya, wajen ganin an bama kowane yaro damar samun ilimi, musamman 'ya'ya matadon dogaro da kai.

Ya bayyanar da matashiyar a matsayin mace mai kamar maza, wajen juriya da kwazo, yana ganin ire-iren ayyukanta, suka kamata matasa a ko ina a duniya suyi koyi da.

Matashiyar dai itace mutun na farko a tarihin duniya, mai kananan shekaru da aka karrama da wannan lambar yabon. An bata wannan kyautar ne a lokacin da take ‘yar shekaru 17 dai haihuwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG