An Sace Jariri Dan Watani hudu

Rundunar ‘yan sandan jahar Abia, ta na neman wani mutun mai suna Uchenna ruwa a jallo a dalilin sace wani jariri dan watani hudu da haihuwa.

Bincike ya nuna cewa Uchenna, bayan da ya sace jariri say a baiwa budurwarsa mai suna Kelechi Uche, domin ta sayar da shi.

Kwamishinan ‘yan Sandan jahar ta Abia Joshak Habila, da yake nuna ta ga jama’a, a Umuahia, babban birnin jahar ta Abia, yace jama’ar, garin ne suka kamata a lokacin datake kokarin sayarda jaririn.

Ya kara da cewa da jami’an ‘yan Sanda suka tuhumeta sai ta bayyana cewa saurayinta mai suna Uchenna da wasu mutane hudu ne suka bata jariri, ta kuma shaidawa ‘yan Sanda cewa kafin a kawo jariri gareta an fara ajiye shi a gida wata mata mai suna Mrs. Love Chinkata, wace itama ake nema a yanzu haka.