Aston villa na matukar farincikin marabatar dan wasan gaba Darren Bent a yayin da kulob din ke daf da shiga satin karshen gama kakar wasan zakaru na premier league a cewar manajan kulob din.
Tim Sherwood ya kara da cewar samun Darren Bent a kulob din Aston Villa a yayin da kulob din ke yunkurin kaiwa satin karshe na kakar wasan zakarun premier league zai zama da muhimmanci kwarai da gaske.
Kulob din Villa dai na fama da matsalar wasan gaba yayin da yake da kwallaye 19 kacal a wasanni 30 na wasan zakarun premier league, wanda yasa shine a baya a cikin rukunin wadanda ke tafe daga lokacin da Sherwood ya maye gurbin Paul Lambert ranar 14 ga watan fabarairu.
A hirar sa da wata kafar sadarwa mai suna Birmingham mail, Sherwood ya bayyana cewa “hakika Bent ya kware wajan jefa kwallo a raga da zarar ya sami dama baya wasa da ita, dan haka zanso in same shi a kulob din Ashton Villa a yanzu haka.”