Babban Bankin Najeriya Na Yunkurin Samar Da Matasa Kwararru

Hada hadar hanayen jari a Najeriya.

A wata sabuwa kuma, Babban Bankin Najeriya ya ce zai karkatar da wani sashi na makudan wuri-na-gugar wurin nan har tala biliyan 1.1, wanda aka ware don habbaka kanana da matsakaitan masana’antu, don daukar nauyin shirin nan na bunkasa rawar da matasa ke takawa a bangaren mai da iskar gas.

Shugaban Anabel Group Nicholas Okoye, ya ce hakan zai taimaka ma matasa da mata, kuma zai samarwa matasa ‘yan Najeriya kwararru aikin yi a wani matakai da aka wa lakabi da YESNIGERIA.

Tuni dai Ministan hadahadar kasuwanci, Olusegun Aganga yay aba da wannan yunkuri yana mai cewa ya kamata a bunkasa harkar man fetur da iskar gas a tushen mutane.

Bincike ya nuna cewa fannin ya na fama da rashin sabbin jinni yayin da wadanda ke aiki a wurin yanzu shekarunsu sun ja.

Har ila yau wani bincike da mujallar Oil Review Africa ta buga ya nuna cewa karancin ma’aikata zai shafi har fannin hadahadar kudade idan har ba a dauki matakan da suka kamata ba.