Kungiyoyin matasa daga addinai daban daban da kabilu daban daban a jihar Plateau, sun gudanar da taro domin yin huduba wa junansu kan zaman lafiya.
Taron wanda aka gudanar a zauren taro na babban Masallaci birnin Jos, ya tattaro kan matasa Musulmi da Kirista da ‘yan kabilar Igbo, da malaman addinai da jami’an tsaro, inda suka kara jaddadawa junansu kasancewa tsintsiya madauri daya da samun zaman lafiya da ci gaba.
Shugaban matasa Musulmi dake cikin garin Jos, Bashir Shuaibu Jibrin, yace makasudin taron shine domin jaddada zaman lafiya, domin irin abubuwan da suka faru a rana sha hudu 14, watan nan na Satumba, ya tsoratar da jama’a, sosai shi yasa mabiya addinan biyu suka ga cewa yakamata a kira taro domin wanzuwar zaman lafiya, da kuma wadanda abin ya shafa kai tsaye wato kabilar Igbo, babu matsayar da ta wuce zaman lafiya.
Ya Kara da cewa an samu hadin kai da cigaba tsakanin matasan Musulmi da na Kirista, a Jos, ana kuma tuntubar juna domin duk wani abu da ya tazo za a iya yin maganinsa.
Sima shugaban kungiyar matasan Kirista, a karamar hukumar Jos, ta arewa Patrick Dutse, yace kowane dan Adam yana bukatar dan uwa wajan cigaba don haka dole matasa su kaucewa shaye shaye dake sasu tada hankali.
Yana mai cewa babban abinda zai taimakawa matasa domin zaman lafiya shine zaman banza baya biyan bukata rashin hankali baya biya bukata shaye shaye baya biyab bukata dole nbe matasa a dukufa kan sana’a.
Shi kuwa Kingsley Dickson, wanda ya wakilci matasan kabilar Igbo, a wajen taron yace hadin kan jama’ar Najeriya, shine hadin kan kasar, yace kuskuren da mutane keyi shine na kallon yana mai cewa Allah ne ya yi mu inda muke saboda haka a cewarsa Najeriya, ita yakamata mu sa a gaba wanda a cewarsa idan aka hada kai Najeriya zata zama daya kuma za a samu ci gaba.
Kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar Plateau, Captain Umar Adam, ya gargadi jama’a dasu kasance masu bin doka saboda haka yace kada saboda banbancin addini ko na kabilanci yasa mu dunga ganin juna kamar abokan gaba.
Your browser doesn’t support HTML5